A ranar 16 ga watan Agustan wannan shekarar ce dai aka faro kakar wasan shekarar 2024/2025 a gasar Firimiyar Ingila, inda akwa yanzu kowace ƙungiya ta samu nasarar buga wasanni 7-7.
Tuni gasar ta soma nisa, inda Liverpool take a saman teburi da maki 18, yayinda Arsenal da Manchester City ke biye mata da maki, 17, kowannen su.
A matsayin matashiya bari muje ga Aminu Halilu Tudun Wada, mai sharhi kan lamuran wasanni.