|
Mahukuntan jamhuriyar Nijar sun shelanta kafa dokar-ta-ɓaci, wanda a ƙarƙashinta gwamnati za ta iya yin amfani da illahirin al’ummar ƙasar da kuma dukiyoyinsu duk lokacin da ta ga ya dace saboda tunkarar barazanar tsaro. Matakin ya zo ne kwanaki ɗaya bayan da Amurka ta ƙaddamar da farmaki kan maɓoyar ƴanbindiga a wani wuri da ke jihar Sokoton Najeriya daf da iyaka da Nijar. Shin ko me za ku ce a game da matakin? Anya hakan zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro da ƙasar ke fama da su? Wannan shi ne maudu'in da muka baku damar tofa albarkacin bakinku a kai. Latsa alamar sauti don sauraren shirin... |