|
Description:
|
|
Jami’an tsaron gandun dajin Jamhuriyar Benin 5 tare da soji 1 suka rasa rayukansu, a yayin da wasu mutane sama da 10 suka samu raunuka, a wani harin kwanton bauna da ‘yan ta’adda suka kai masu a gandun dajin da ya hada kan iyakar kasar, da Burkin Faso da Nijar, kamar yadda mahukumtan kasar ta benin suka sanar a ranar Laraba.
To domin jin ra’ayin masana dangane da yadda yan ta’adda ke ci gaba da fadada a yankunan kurmin yammacin Afrika, Mahaman Salisu Hamisu ya tattauna Dr Sani Yahaya Janjuna, masanin zamantakewa da halayar dan Adam a Jamhuriyar Nijar ya yi mana tsokaci a kai. |