|
Description:
|
|
Wasu cibiyoyin bunkasa dimokiradiya guda biyu da ke Amurka da suka ziyarci Najeriya domin ganin shirin zaben shekara mai zuwa, sun bayyana fargabar cewar, tashe-tashen hankulan da ake samu a kasar na barazana ga shirin zaben baki daya.Cibiyoyin sun bayyana rikicin Boko Haram da kuma na makiyaya da manoma a matsayin wadanda za su iya hana gudanar zaben cikin kwanciyar hankali. Dangane da wannan rahoto, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon ministan 'yan Sandan Najeriya, Dr. Ibrahim Yakubu Lame. |