|
Description:
|
|
Yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke bikin cika shekaru 70 da kafuwa a yau, yanzu haka akwai kasashe fiye da 40 da ke fama da tashe-tashen hankula da suka hada da kasashen Sryia, Yemean, Afghanistan, Libya da dai sauransu wadanda majalisar ta gaza shawo kansu.
Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da shugaban rundunar Adalci a Najeriya Alhaji Abdulkarim Dayyabu a game da irin rawar da Majalisar Dinkin Duniya ke takawa wajen samar da zaman lafiya da warware sauran rigingimun da ake fama da su, ga kuma zantawarsu. |