Search

Home > Wasanni > Yadda aka gudanar da gasar Super 4 ta a Najeriya
Podcast: Wasanni
Episode:

Yadda aka gudanar da gasar Super 4 ta a Najeriya

Category: Sports & Recreation
Duration: 00:09:59
Publish Date: 2026-05-11 07:07:42
Description:

A ranar juma’ar data gabata ne dai aka kammala gasar gasar Super 4, wacce aka fafata tsakacin ƙungiyoyi 4 da suka haɗa da Sporting Lagos da Inter Lagos da Ranchers Bees ta Kaduna sai kuma Doma United, da suka zama zagaru a rukunoninsu na gasar NNL, gasa ta biyu mafi daraja a Najeriya.

An gudanar da gasar ne a yanayin yadda ake gudanar da gasar lik-lik, inda kowa ya kara da kowa ganin cewa kowaccensu za ta haska a gasar Firimiyar Najeriya a kakar baɗi.

A wasannin ƙarshe da aka aka yi, Sporting Lagos ta sha kashi da ci ɗaya mai banshi a hannun Inter Lagos, amma sai dai hakan bai hanata lashi gasar ba da ban-bancin ƙwallaye, domin kowaccensu ta ƙare ne da maki 6.

Wannan ne karo na farko da Sporting Lagos ta taɓa lashe kofin tun bayan samar da ita a shekarar 2022.

Total Play: 0

Some more Podcasts by France Médias Monde

100+ Episodes
Cap Océan I .. 10+     3
100+ Episodes
Kida da Al'a .. 10+    
60+ Episodes
300+ Episodes
Une semaine .. 10+     10+
50+ Episodes
Imprensa 2    
100+ Episodes
100+ Episodes
700+ Episodes