Search

Home > Wasanni > Matsalolin da suka dabaibaye ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jigawa Golden Stars
Podcast: Wasanni
Episode:

Matsalolin da suka dabaibaye ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jigawa Golden Stars

Category: Sports & Recreation
Duration: 00:09:59
Publish Date: 2026-05-04 08:41:06
Description:

A wannan mako shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh ya mayar da hankali ne kan halin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jigawa Golden Stars ke ciki, wanda ya haddasawa ƙungiyar gagarumin koma baya.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Jigawa Golden Stars, ta kasance guda cikin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar ƙwararru da ake ji da su a shekarun baya daga yankin Arewacin Najeriya, wadda ta shafe tsawon shekaru tana gwagwarmaya a gasar firimiyar ƙasar wato NPFL.

Ƙungiyar ta shahara wajen horas da matasan ƴan wasa daga Arewacin Najeriya da kuma fafatawa da manyan ƙungiyoyi a ƙasar. A baya dai ƙungiyar ta Jigawa Golden Stars duk da namijin ƙoƙari da ta ke yi, ta taɓa shafe kusan shekaru bakwai ba tare da zuwa gasar Firimiyar Najeriya, kafin daga bisani ta sake komawa babbar gasar.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

Total Play: 0

Some more Podcasts by France Médias Monde

100+ Episodes
Cap Océan I .. 10+     3
100+ Episodes
Kida da Al'a .. 10+    
60+ Episodes
300+ Episodes
Une semaine .. 10+     10+
50+ Episodes
Imprensa 2    
100+ Episodes
100+ Episodes
700+ Episodes