|
A jiya Lahadi ne dai aka buga wasan ƙarshe a gasar lashe kofin nahiyar Afrika ta AFCON karo na 35 da ƙasar Morocco ta karɓi baƙunci, inda Senegal ta samu nasara da ci 1 da nema kan Morocco, bayan da ɗan wasanta Pape Alassene Gueye ya jefa kwallo jim kaɗan bayan ƙarin lokacin. Wasan ƙarshen ya kasance mai cike da cecekuce sakamakon tsaiko minti 20 da aka samu, sanadiyar bugun daga kai sai mai tsaron gida da aka bai wa Morocco, lamarin da ya fusata ƴan wasan Senegal ficewa daga fili, amma daga baya Sadio Mane ya dawo da su aka ci gaba da fafatawa. Ɗan wasan gaba na Senegal Sadio Mane ne ya lashe gwarzon ɗan wasa a wannan gasa, Yassine Bounou na Morocco ya lashe gwarzon mai tsaron raga shima abokin wasansa Brahim Diaz da ya zubar da bugun daga kai sai mai tsaron gida ya lashe kyautar takalmin zinari da kwallaye 5. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh............ |