|
Description:
|
|
Shirin awannan mako zai maida hankali ne kan yadda aka soma kakar bana ta manyan gasannin kwallon kafa na duniya, wato Firimiyar Ingila, La Ligar Spain, da League one na Faransa. Tuni dai aka soma manyan gasannin kwallon ƙafa a Duniya, inda aka fara fafata wa a gasar Firimiya, kuma zakarun gasar Liverpool suka karya kumallo da Bounmouth da kwallo hudu da biyu, yayinda itama Manchester city suka yi wa Wolves dukan sakwarar legas da kwallo hudu da nema, ita kuwa Manchester United kashi ta sha a gida a hannun Arsenal da ci daya mai ban haushi koda dai Chelsea anata bangaren duk da cefanen da tayi lamarin baizo mata da kyau ba a karawar su da Cristal Palace. |