Search

Home > Wasanni > Salah ya shafe tarihin Thierry Henry na yawan jefa kwallo a gasar Firimiya
Podcast: Wasanni
Episode:

Salah ya shafe tarihin Thierry Henry na yawan jefa kwallo a gasar Firimiya

Category: Sports & Recreation
Duration: 00:09:59
Publish Date: 2025-01-27 10:15:43
Description:

Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokacin ya ziyarci gasar Firimiyar Ingila ne don duba sabon tarihin da ɗan wasan Liverpool Mohammed Salah ya kafa a gasar. Mohammad Salah dai a yanzu ya shafe tarihin Thierry Henry na zura kwallaye 175 a gasar Firimiyar Ingila, bayan da ya jefa kwallo a karawar da suka yi da Ipswich.

A yanzu dai Mohammed Salah ne na 7 a jerin ƴan wasan da a tarihi suka fi yawan jefa kwallo a raga a babbar gasar ta Ingila.

Ƴan wasan da a tarihi suka fi yawan jefa kwallo a gasar dai su ne Alan Sheare mai  kwallaye 260 da Harry Kane  213 da Wayne Rooney 208 da Andrew Cole 187  da Sergio Agüero 184 da Frank Lampard 177 sai shi Mohamed Salah 176 ya yinda a yanzu Thierry Henry  mai kwallaye 175 ya koma mataki na 8 a wannan jeri.

Ƙu latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.........

Total Play: 0

Some more Podcasts by France Médias Monde

100+ Episodes
Cap Océan I .. 10+     3
100+ Episodes
Kida da Al'a .. 10+    
60+ Episodes
300+ Episodes
Une semaine .. 10+     10+
50+ Episodes
Imprensa 2    
100+ Episodes
100+ Episodes
700+ Episodes