Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan lokacin yayi nazari ne akan wasannin matakin dab da na kusa da na karshe wato na zagayen Kwata final da aka yi a gasar AFCON.
Yanzu haka dai kasashe hudu ne suka rage a gasar ta cin kofin kasashen nahiyar Afirka da kasar Ivory Coast ke karbar bakunci, bayan wasannin da aka fafata a ranakun Juma’a da Asabar.