|
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya yi duba kan yadda a wasu lokuta magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa a Najeriya ke janyowa kungiyoyin da su ke goyawa baya gagarumar koma baya a wasu lokutan har da tara ko zaftare maki. Karkashin firimiyar Najeriya ko a kakar da ta gabata sai da manyan kungiyoyi suka fuskanci hukunci daga hukumomin gasar a dalilin rikici yayin wasanni wanda ya kai ga zaftare makin Kano Pillars guda cikin wadannan kungiyoyi. Wannan matsala dai ba sabon abu ba ne a gasar ta Firimiyar Najeriya lura da cewa a kusan dukkanin kaka akan samu faruwar wannan matsala. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin... |