|
Shirin a wannan makon na musamman ne wanda ya yi duba gameda gasar lashe kofin duniya ta mata da aka kammala.Wannan ne karo na farko da kasashe biyu suka karbi bakuncin gasar lashe kofin duniya ta mata, kuma aka kara yawan kasashen da ke halartar gasar daga kasashe 24 zuwa 32. Kasashen Spaine da Ingila ne suka samu nasarar kaiwa wasan karshe, inda kasar Spain ta samu nasarar lashe gasar, inda kasar Ingila ta kare a mataki na biyu, ita kuma kasar Sweden tazo na uku, sai kuma kasar Austria daya daga cikin masu masaukin baki ta kare a mataki na hudu. |