|
Description:
|
|
Shirin Duniyar wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya leka garin Mai Tsidau ne a Karamar hukumar Makodan Jihar Kano ta arewacin Najeriya, dan kawo muku yadda wata baiwar Allah mai suna Coach Fatima, wadda ta zamo mace daya tilo da ke horas da kungiyar kwallon kafa ta maza, wadda zancen nan da ake tuni labarinta ya karade kafafen sada zumunta a Najeriya.
Shekaru hudu da suka gabata ne dai coach Fatima ta fara aikin horas da wadannan matasa, bayan rasuwar me gidanta, a wani yanayi na cimma burin da ta ke dashi tun ta na karama.
To dangane da hakan wakilin mu Abubakar Isa Dandago ya ziyarci filin da Kociya Fatima ke bada horon a karshen mako.
Domin jin cikakken shirin ku latsa alamar sauti...... |