|
Description:
|
|
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan makon ya yi nazari ne kan irin ci gaban da kasar Senegal ke samu a ‘yan shekarun da suka wuce a harkar wasan kwallon kafa a duniya.
A baya-bayan nan ne dai, Senegal ta zamo kasa ta farkoa nahiyar Afrika da ta lashe manyan kofuna 3 da ake fafatawa a kan su.
Hawa wannan mataki kuwa da Senegal ta yi, ya biyo bayan lashe gasar cin kofin nahiyar Afrika ta ‘yan wasan cikin gida da ake yi wa lakabi da CHAN, bayan ta doke kasar Algeria da ta yi ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida, kamar yadda ta lallasa kasar Masar nan ma ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida, lamarin da ya basu damar daukar kofin nahiyar Afrika wato Nations Cup, ga kuma kofin gasar rai-rai na Afrika da kasar ta lashe a baya-bayan nan.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin...... |