|
Description:
|
|
Shirin "Duniyar Wassani" na wannan makon ya leka ne Jamhuriyar Nijar inda ake ci gaba da fafatawa a gasar lik din kasar.
An kammala wasan zagaye na farko a gasar lik din Jamhuriyar Niger, da kungiyoyi 14 ke fafatawa a cikin ta.
Gasar ta bana ta fuskanci tsaiko da dama ganin yadda a tsakayar ta aka tafi hutu don halartar gasar CHAN, sannan kuma aka sake bada hutu ga 'yan wasa bayan kammala gasar.
Haka nan kuma gasar na fuskantar rashin samun 'yan wasa daga kasashen waje, ga rashin wadatattun kudin da ake gudanar da gasar su wanda kuma ke kara rage mata armashi.
Sai dai duk da kalubalen da ake fuskanta, gasar na samun ci gaba musamman idan aka yi la'akari da yadda aka gyara dukkanin filayen wasanni da ake buga gasar a cikin su, da kuma farfadowar da kananan kungiyoyi ke yi wajen samun tagomashi. |