|
Description:
|
|
Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako zayyi bitar gasar motsa-jiki na zaratan da ke kare dajin daga farauta da kiwo ko sarar itatuwa wanda ake kira da Wildlife Ranger Challenge a Turance.
Gasar wacce ake gudanarwa kowacce shekara masu kare dazuzzukan yawon bude-ido ne ke gudanar da ita.
A wannan shekarar, daruruwan masu tsaron dazukan Afrika ne daga kasashe sama da 20 suka shiga gasar domin samun kyaututtukan yabo da kuma karin kuzarin gudanar da aikin su na kare daddobi da muhallin su. |