|
Description:
|
|
Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon ya yi mana dubi ne a kan yadda hamayya ke ci gaba da zafafa tsakanin magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da na Katsina United. Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata ne aka ci Kano Pillars tara bayan da magoya bayanta suka lalata mata motar da ke daukar 'yan wasanta. Shirin ya tattauna da masana masu bibiyar wasannin kwallon kafa a Najeriya a kan dalilan da suka ta'azzara wannan mummunar hamayya da ya ke zama hadari ga harkar tamaula. |