|
Description:
|
|
Hukumar kwallon kafar Afrika ta sanar da dage haramci da ta yi na soke wasanni a filin wasa na Olembe biyo bayan mutuwar mutane 8 da aka samu ranar litinin 24 ga watan janairu 2022.
Masar ta yi waje da kungiyar Morrocco da ci 2 da 1, wasar da aka bayyana cewa an baiwa hammuta iska tsakanin yan wasan na Masar da Morrocco jim kadan da kammala ta ,bayan da yan wasan suka fice daga fili.
Kungiyar kwallon kafar Sanegal ta samu tsallakawa mataki na ga ba ,bayan doke kungiyar kwallon kafar Equatorial Guinee da ci 3 da 1,Sadio Mane da abokanin tafiyar sa za su kara da kungiyar kwallon kafar Burkina Faso ranar laraba.
A bangaren kungiyar kwallon kafar Burkia Faso,mai horar da wannan kungiya mai suna Kamou Malo,da samun nasara a faffatawa da kungiyar Tunisia,ya na mai cewa al’amari ne yan kasar ga baki, jajircewa da juriya suka yan wasan ga samun wannan nasara,abin farin ciki ne ga Burkina Faso.
Abdurahamane Gambo daga Yaounde ya hada mana shirin Duniyar wasanni. |