|
Description:
|
|
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi nazari ne kan cece-kucen da ake yi kan kura-kuran da na'urar VAR ke tafkawa a yayin taimaka wa alkalin wasa yanke hukunci. A baya-bayan nan Hukumar Kwallon Kafar Ingila ta amince cewa, na'urar ta yi kuskure wajen bada bugun fanariti a wasu wasannin da aka yi a makon jiya a gasar firimiyar kasar. Kazalika shirin ya yi fashin-baki kan sabon jadawalin gasar zakarun Turai a matakin kwata-fainal, inda Real Madrid ke fuskantar barazanar rasa gurbi. |