|
Description:
|
|
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya sake waiwayar wainar da ake tuyawa a Gasar Cin Kofin Duniya ta Matasa 'yan kasa da shekaru 17 da ke gudana a Brazil, inda kasashe irinsu Najeriya da Brazil mai masaukin baki da Faransa da Angola da Senegal suka samu gurbi a zagaye na biyu na gasar. Shirin ya kuma duba kalubalen da ke gaban gasar firimiyar Najeriya a daidai lokacin da aka fara gudanar da ita a karshen mako. Kazalika za ku ji fashin bakin masana dangane da koma-bayan da Barcelona da Real Madrid ke fuskanta a kakar bana. |