|
Description:
|
|
A yau shirin duniyar wasannin zai maida hankali ne akan sabon tsari ko gyaran fuskan da aka kawowa gasar yan rukuni na daya na kwallon kafa a Jamhuriyar Nijar.
Hukumar kwallon kafa Jamhuriyar Nijar Fenifoot ta tsaida ranar 22 ga wannan wata na Disemba ne za a koma kwambala ta kasa bayan kammala kakar bara, sai dai maimakon kungiyoyi 14 kamar yadda aka saba, a wannan karo Ligue Airtel ta Nijar za ta koma 16, daga cikin kungiyoyin da suka samu hawa rukunin na farko akwai, Espoir ta Damagaram sai kuma kulob daya na Doso da zai fito bayan karawa tsakanin Tagur da Entente. |