|
Description:
|
|
A jamhuriyar Nijar hukumar kwallon kafa ta Fenifoot ta aiwatar da sabon tsari na samar da gidaje a matsayin Ofis zuwa kungiyoyin Ligue na kasar.
Sanarwa daga Shugaban hukumar Fenifoot Kanal Djibrilla Hima a wata ziyara da ya kai Maradi tareda ganawa da masu ruwa da tsaki a harakokin kwallon kafa na yankin.
A cikin shirin Duniyar wasanni tareda Abdoulaye Issa za ku ji irin ci gaba da aka samu a bangaren kwallon kafa dama shirin da hukumomin ke yi wajen karbar bakuncin gasar cin kofin Afrika na yan kasa da shekaru 20.
|