|
Description:
|
|
Shirin duniyar wasanni na wannan makon tare da Abdurrahaman Gambo Ahmad ya tattauna ne kan shirye-shiryen kasashen duniya game da gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakwanci nan da kwanaki kalilan masu zuwa. Najeriya na daga cikin kasashen da tuni suka sanar da 'yan wasan da za su wakilce su a gasar. Shirin ya kuma tattauna kan irin rawar da mai tsaren ragar Italiya da kungiyar Juventus, Gianlugi Buffon ya taka a fagen tamaula a duniya bayan ya sanar da rataye takalmansa a makon jiya a Juventus. |