|
Description:
|
|
A cikin shirin duniyar wasanni,Abdoulaye Issa ya mayar da hankali zuwa dan wasa Cristiano Ronaldo da ya canza kungiya daga Real Madrid zuwa kulob na Juventus de Turin na kasar Italiya.
Manazarta na ci gaba da sharhi a kai, banda haka mu leka duniyar gasar cin kofin Duniya a kasar Rasha, ranar Lahadi ne za a yi karawr karshe tsakanin Faransa da Crotia dangane da gasar cin kofin Duniya na kwallon kafa.
Hukumar Fifa ta FIFA ta fitar da sunan alkali da zai wakilci karawa tsakanin Faransa da Crotia,shine dan kasar Argentiana Nestor Pitana. |