|
Description:
|
|
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne game da matakin da Hukumar Shirya Gasar Lig ta kasar da tauka na dakatar da gasar a bana tare da mika kofi ga kungiyar Lobi Stars duk da cewa ba a kammala gasar ba, matakin da masharhanta ke cewa zai yi mummunan tasiri a tsarin shirya gasar. Kazalika shirin ya tattauna kan matakin dakatar da kocin Super Eagles Salisu Yusuf har na tsawon shekara guda tare da cin sa tarar Dala dubu 5 kan samun sa da karbar cin hancin dubu 5. |