|
Description:
|
|
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne game da sake zaben Amaju Pinnick a matsayin shugaban Hukumar Kwallon Kafar Najeriya wanda a karon farko kenan cikin sama da shekaru 60 da wani shugaban na NFF ke zarcewa a mukaminsa. Sai dai zaben na zuwa a yayin da wasu ke tantama kan ingancinsa biyo bayan kalubalantar sahihancin shugabancin Pinnick a kotu, ko da dai mahukuntan Najeriya sun nuna bangaren da suka karkata bayan Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya ta yi barazanar dakatar da kasar daga harkokin wasannin kwallon kafa. |