|
Description:
|
|
Shirin 'Lafiya Jari Ce' a wannan makon ya duba batun illolin cutar sukari ko kuma diabetes a turance, cutar da bisa al’ada ake gudanar da bikin yaki da ita a kowacce ranar 14 ga watan Nuwamba a wani yunkuri na wayar da kan jama’a game da illolinta dama yadda za a kare kai daga kamuwa da ita.
A daidai lokacin da duniya ke bikin ranar masu fama da cutar ta siga ta duniya (WDD), masana sun nuna damuwa cewa akalla ‘yan Najeriya miliyan shida ne suke dauke da ita, ma'ana – daya dag cikin manyan mutane 10– ke fama da ciwon suga, duk da cewa adadin zai rubanya nan da shekarar 2030, tare da al’ummar kasar. |