|
Description:
|
|
A wannan lokaci da annobar Covid 19 ke ci gaba da kisa ,hukumar UNICEF na gargadi zuwa iyayen yara na ganin sun mayar da hankali don bayar da kulawa da ta dace ga yaran su.
A Najeriya,kungiyoyi da iyaye na ci gaba da kira ga hukuma don samun kayaki na zamani da jami'an kiwon lafiya da suka dace da zasu taimaka don takaita yaduwar anobar da ma wasu matsalloli da suka jibanci kiwon lafiya.
Azima Aminu ta duba labarin da ya shafi asusun tallafawa yara kanana na UNICEF a cikin shirin lafiya jari ce.
|