|
Description:
|
|
Daga cikin batutuwan da shirin Dandalin nishadi ya tattauna akai akwai yadda tauraron fina-finan Hollywood dake Amurka Will Smith ya lashe kyautar gwarzon jarumi na bana da yafi kowa nuna bajinta a matsayin acta, saboda rawar da ya taka a matsayin mahaifin fitattun 'yan wasan tennis na duniya Venus da Serena Williams a wani sabom fim da King Richard.
Sai dai Smith ya yi abin ba za ta a wajen bikin, inda ya je ya shararawa mai gabatar da shirye shirye Chris Rock mari saboda abinda ya kira shaguben da ya yi wa iyalinsa. |