Search

Home > Kasuwanci > Yadda matsalolin tsaro ke kassara kasuwanci a arewacin Najeriya
Podcast: Kasuwanci
Episode:

Yadda matsalolin tsaro ke kassara kasuwanci a arewacin Najeriya

Category: News & Politics
Duration: 00:10:00
Publish Date: 2026-04-08 11:03:29
Description:

Shirin na wannan makon ya mayar da hankali ne kan irin fargabar da 'yan kasuwar arewacin Najeriya da ke fatauncin kayayyaki zuwa wasu sassan jihohi ke ciki, sakamakon ayyukan bata gari da ke tare hanya wanda a wasu lokuta kan kai ga rasa rayuka.

Abune da aka saba gani, ‘yan kasuwar dake hada Hada tsakankin jihohi daga wannan kasuwa zuwa waccan ko tsakanin kasuwannin kauyuka.

To sai dai Kuma irin wannan tsarin na fuskantar cikas ko koma baya, alal misali ga yan kasuwa a jihar filato dake arewacin Najeriya, sakamakon munanan halaye na wasu bata gari marasa tausayin rayuwar Dan Adam, dake tare Yan tireda ko Kuma matafiya inda suke Kai musu farmaki, tare da yi musu kisan gilla.

A kwanakin baya wasu Bata gari sun tare wasu Yan kasuwa da ke fatauci daga garin Jos zuwa yankin kudancin Jihar, inda suka kashe biyar daga cikinsu, Wannan  al’amari ya Sanya Yan Kasuwar da sauran matafiya shiga hali na fargaba a kowane yanki dake jihar.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

Total Play: 0

Some more Podcasts by France Médias Monde

100+ Episodes
Cap Océan I .. 10+     3
100+ Episodes
Kida da Al'a .. 10+    
60+ Episodes
300+ Episodes
Une semaine .. 10+     10+
50+ Episodes
Imprensa 2    
100+ Episodes
700+ Episodes
500+ Episodes
Eco d'ici Ec .. 8     7