|
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya yi dubi ne kan wani sabon yunkuri na kara inganta alakar kasuwanci tsakanin Najeriya da Nijar inda hukumar kwastom a jamhuriyar Nijar tayi tattaki zuwa Najeriya don tattaunawa hanyoyin da za’a bi don saukaka hada-hadar kayayyaki tsakanin kasashen biyu. Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam na Najeriya Adewale Adeniyi, ya sake jaddada aniyar Hukumar na sauƙaƙe cinikayya a yankin, ta hanyar saukaka jigilar kayayyaki da kuma haɓaka haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen da ke makwabtaka da su, musamman Jamhuriyar Nijar. Adeniyi ya bayyana hakan ne a ranar Juma'ar da ta gabata, yayin wani babban taron haɗin gwiwa tsakanin Hukumar Kwastam ta Najeriya da takwararta ta Jamhuriyar Nijar, ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar, Muhammadu Yaqouba, da aka gudanar da hedikwatan Kwastam da ke Maitama a Abuja. Tawagar Nijar ta kunshi shugabannin cibiyar inganta kasuwanci na Nijar wato Chamber des Commerce. Cikin mahimman abubuwan da aka duba a ganawar akwai saukaka zirga-zirga a kayan a iyakokin kasashen biyu ciki harda jigilar man metur na kamfanin Dangote, hakazalika za’a bada damar wucewar wasu kayayyaki da suka makale a bodar Kamba na jihar Kebbi, tireloli 1,600, da suka kwashe sama da watanni 2. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin. |