|
Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole"na wannan mako tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan sabbin kiraye-kirayen da Bankin Duniya da kuma Asusun bada Lamuni na Duniya (IMF) suka yi ga gwamnatin Najeriya wajen ganin ta ɗauki matakab da suka kamata don ƙara rage hauhawar farashin kayayyaki domin al’umma ta amfana a zahiri da kuma ci gaban tattalin arziki ƙasar. Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Ƙasa da Ƙasa, IMF, sun bayyana cewa har yanzu tattalin arziƙin Najeriya bai kai matsayin da za a ce ya daidaita ba, duk da wasu sauye – sauye da gwamnati ke aiwatarwa. Hukumomin sun ce rashin daidaiton tattalin arziƙin na ci gaba da shafar rayuwar jama’a, musamman ta fuskar hauhawar farashin kayayyaki. Masana tattalin arziƙi sun goyi bayan gargadin da Asusun Ba da Lamuni na Ƙasa da Ƙasa, IMF, ya yi kan cewa sauye-sauyen tattalin arziƙin da ake aiwatarwa a ƙasashe masu tasowa, ciki har da Najeriya, na iya fuskantar barazana idan ba a tabbatar da dorewarsu ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin. |