Shirin "Duniya Akai Miki Dole" tare da Faruk Muhammad Yabo a wannan mako ya yi duba ne kan sabbin harajin da gwamnatin Najeriya ke shirin karɓa a hannun jama'ar ƙasar, a wani yanayi da ƙasar ke fatan tattara wani ɓangare na kuɗaɗen tafiyar da harkokinta.
Shirin a wannan mako ci gaba ne na makon da ya gabata dangane da wannan dokar haraji wadda al'ummar Najeriya ke ci gaba da suka akanta.
A cikin shirin akwai tattaunawa da ƙwararru a fagen na tattalin arziƙi waɗanda da dama suka yi suka ga sabon tsarin harajin na shugaba Tinubu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.