Shirin kasuwa a kai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya mayar da hankali kan matsi da tsadar rayuwa da kuma yadda wannan matsala ta jefa kaso mai yawa na magidantan Najeriya a halin tsaka mai wuya, matsalar da ke da nasaba da sabbin manufofin gwamnati ciki har da ƙarin farashin man fetur.