Shirin Kasuwa akai miki Dole tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan noman albasa da tafarnuwa a jihar Sokoto ta arewacin Najeriya, jihar da ke matsayin kan gaba wajen noman albasar da tafarnuwa a kasar.
Wani kalubale ga manoman na Albasa da Tafarnuwa a jihar ta Sokoto shi ne yadda ake fuskantar lalacewarta musamman a lokacin bozonta, wannan dalili ya sanya samar da wasu dabarun adana ta don kaucewa asarar da manomanta ke fuskanta.
Ku latsa alamar sauti don saurarin cikakken shirin..........