|
Description:
|
|
Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya maida hankali ne kan kaddamar da katafariyar matatar Man Attajirin Afirka Alhaji Aliko Dangote a anguwar Lekki dake birnin Legas a kuduncin Najeriya.
A wannan Litinin 22 ga watan Mayun 2023 ne akayi bukin kaddamar da matatar mai komai da ruwanka mafi girma a duniya, a anguwar Ibuju Lekki dake birnin Legas, wanda ya zo mako guda kafin bukin mika mulki ga zabebben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Matatar mai girman kadada 2,635 zai rika tace danyen mai ganga dubu 650 kowace rana, amatsayin « single train » mafi girma a duniya, duba da cewa, tana iyi tace kusan daukacin albarkatun da ake cirewa daga danyen mai, ciki harda man fetir da na Dizal da man jiragen sama da kalanzir da gas din girki da dai sauransu.
.Attajirin Nahiyar Afrika Alhaji Aliko Dangote, wanda ya gina matatar, yace ya shiga harkokin ne domin saukaka tsadar man fetur da ‘yan kasar kimanin miliyan 200 ke fama da shi da kuma samar da ayyukan yi a kasar mafi girma a nahiyar Afirka. |