|
Description:
|
|
Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba ya yi duba kan tsananin tsadar tumatir da ake gani a sassan Najeriya musamman yankin kudancin kasar wanda ya dogara da yankin arewaci gabanin samun kayan gwari inda rahotanni ke cewa farashin kwandon tumatur ya ninka fiye da sau 3 na farashin da aka saba sayen shi a baya.
Wasu dai alakanta tashin farashin tumaturin da yadda gonakinsa musamman a arewacin kasar da ke nomansa suka gamu da ibtila'in cutuka da suka kassara yadonsu baya ga haddasa asara ga manoma.
Wasu bayanai sun ce farashin tumaturin ya kai dubu 70 a wasu yankuna na kudancin Najeriya, lamarin da ba a saba gani ba.
Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin................. |