|
Description:
|
|
Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya maida da hankali ne kan karancin tsabar kudi a hannun ‘yan Najeriya sakamakon wa’adin daina amfani da wasu takardun kudin kasar Naira da babban bankin kasar CBN ya sauyawa fasali, lamarin da yasa wasu yankunan kan iyakokin kasar suka fara amfani da takardun kudin CFA.
Yanzu haka wasu yankunan Najeriya da sukayi iyaka da jamhuriyar Nijar da Kamaru da Benin sun karfafa amfani da takardun kudin CFA, saboda karancin Naira.
Mazauna wadanan yankuna irin Sokoto da Zamfara da Lagos da Kwara da Adamawa da Taraba da Cross River da dai sauransu suka ce suna hada-hada da kudin CFA ne saboda rashin tabbas da Naira ya shiga.Yayin da a wasu yankuna ma aka fara amfani da tsarin bani gishiri in baka manda.
|