|
Description:
|
|
Shirin Kasuwa a Kai Miki Dole na wannan makon ya mayar da hankali ne a game da taron shugabannin kamfanoni da manyan ‘yan kasuwa na Afirka da aka gudanar tsakanin ranakun 13 zuwa 14 na watan Yunin wannan shekara ta 2022 a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast.
Taron na bana ya samu halartar ‘yan kasuwa sama da dubu daya da 800, tare da wasu shugabannin kasashen Afirka, da suka hada da Alassan Ouattara na Cote d’Ivoire mai masaukin baki, Macky Sall na Senegal, da Mohamed Bazoum na Jamhuriyar Nijar da kuma mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin tare da Ahmed Abba |