|
Description:
|
|
Shirin "Kasuwa Akai Miki Dole" tare da Ahmed Abba ya leka ne wata kasuwa a jahar Cross river dake kudu maso gabashin Najeriya, inda har yanzu ake cinikin bani gishiri in baka manda, ko kuma cinikayya ba tare da hada-hadar kudi ba, wanda ake kira "trade by barter" a turance.
Kasuwar al’ummar Esuk Mba da ke karamar hukumar Akpabuyo a jihar Cross River na ci gaba hadahadar kayan abinci ta hanyar cudeni-incudeka tun daga lokacin da aka kafa ta a shekarar 1956, zuwa yanzu.
Kasuwar dake ci mako-mako ana bude hada-hada tun daga karfe 7 na safe, zuwa tsakar rana ta kowace Asabar.
Mutan ƙauyukan kan kwashi kayan da suke amfani da su zuwa kasuwar domin musanya da wanda suke bukata. |