|
Description:
|
|
Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya maida hankali ne dangane da ziyarar da karamin Ministan Faransa mai kula Kasuwancin Kasashen Waje, Franck Riester, ya kawo Najeriya da zummar karfafa alakar kasuwanci tsakanin kasashen biyu da kuma mika goran gayyata ga mahalarta manyan taruka biyu na tattalin arzikin Afrika- Faransa da shugaba Emmanuel Macron zai dauki nauyi a watan Mayu da kuma Yuli mai zuwa.
Hada-hadar Mai ita ke kan gaba a harkokin kasuwanci tsakanin Farasa da Najeriya, inda acikin watan Satumba, kamdfanin Axens na Faransa ta rattaba hannu a wata yarjejeniyar hadin gwiwa da takwaransa a Najeriya BUA na hamshakin attajiri Alhaji Abdul Samad Rabi'u don gina matatar mai a jihar Akwa Ibom dake kudu maso kudancin Najeriya.
Yayin da Hamshakin attajirin da yafi kowa kudi a Afrika da bakar fatar Duniya Alhaji Ali Dangote yace, yanzu haka sun kulla sabuwar yarjejeniya don farfado da kamfanin kerar motoci na Peugeot a Najeriya. |