|
Description:
|
|
Shugabannin asibitoci a Najeriya sun gabatar da korafi a kan yadda kamfanonin inshoran lafiya ke kin biyan su kudaden inshoran lafiyar da suke karba daga hannun gwamnatoci da kuma kamfanoni domin kula da ma’aikatansu.
Shugabannin sun ce suna bin irin wadannan kamfanonin dimbin bashi yayin da su kuma tuni suka karbi kudaden daga hannun gwamnati dan biyan su, inda suke barazanar kin kula da ma’aikatan da basu da lafiya.
Dangane da wannan matsayi, mun tattauna da Farfesa Balarabe Sani Garko, tsohon Sakatare Janar na kungiyar likitoci kwararru na Afirka ta Yamma kuma malami a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ga tsokacin da yayi a kai. |