|
Description:
|
|
Gamayar kungiyoyin kwadago na fannin ilimin boko a kasar Nijar sun shiga wani yajin aikin jan hankalin gwamnati na tsawon kwanaki 2 daga yau Litinin don nuna rashin jin dadinsu game da saba alkawarin da gwamnati ta yi kan hakkokinsu da dama da suka sanya ma hannu a baya a ciki har da maganar daukan malaman kwantiragi aiki a matsayin na dindindin, da sauransu.
Wannan yajin aiki a iya cewa shine mafi girma da wannan gwamnatin ta fuskanta tun bayan da shugaba Bazoum ya dare kan karagar mulkin kasar.
Ibrahim Malam Tchillo ya tattauna da Gali Dauda, Sakataren Kungiyar Malaman, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana. |