|
Description:
|
|
Matasalar rashin tsaro na cigaba da ci wa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya, sakamakon yadda ‘yan bindiga da aka ayyana a matsayin ‘yan ta’adda ke ci gaba da kai hare-hare, duk da kokarin da gwamnati take yi wajen kaddamar da farmaki akansu da zummar kawo karshen ta’addancin da suke aikatawa a sassan kasar, musamman ma a yankin arewa maso yammaci da kuma arewa ta tsakiya.
Kan sha’anin tsaron ne Garba Aliyu Zaria ya tattauna da Hajiya Naja’atu Bala Muhammad fitacciyar ‘yar Siyasa a Najeriya. |