|
Description:
|
|
Gwamnatin Mali ta bukaci zaunawa da Faransa domin sake bitar yarjejeniyar tsaro da ke tsakanin kasashen biyu, a daidai lokacin da alaka ke kara yin tsakanin mahukuntan birnin Paris da na Bamako.
Firaministan Mali Choguel Maiga ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wadda babu adalci a cikinta, domin kuwa a karkashin yarjejeniyar, Mali ba ta iya ratsa sararin samaniyarta sai tare da amincewar Faransa.
To domin jin karin bayani a game da wannan yarjejeniya ta tsaro, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Tahirou Guimba, wanda tsohon jami’in tsaron jandarma ne a jamhuriyar Nijar, ga kuma zantawarsu. |