|
Description:
|
|
Wata tawagar manyan jami’an gwamnatin Chadi karkashin jagorancin ministan tsaro kasar Daoud Yaya Brahim ta gana da shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustine Archange Touadéra a birnin Bangui. Babban daliin wannan ganawa shi ne yadda za a sake bude iyakar kasashen biyu, wadda aka rufe tun 2014 a lokacin mulkin shugaba Idris Deby.
Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Idris Adamu Sarkin Hausawa daga kasar ta Chadi, dominm jin muhimmancin sulhuntawa tsakanin Chadi da makotanta. |