|
Description:
|
|
Kungiyar Kwadago Najeriya ta sanar da soma yajin aikin gama-gari tun daga wayewar gari yau Alhamis har sai iabinda hali yayi, domin neman gwamnati ta yiwa ma’aikata karin albashi mafi kankanta a kasar.
A taron manema labarai a Abuja, gamayyar kungiyar kwadagon ta Najeriya, ta bayyana cewa matakin nasu ya biyo bayan rashin gamsuwa ne da take-taken gwamnati dangane da cika alkawarin da ta dauka.
Garba Aliyu Zaria ya nemi karin bayani daga bakin Comrade Nasir Kabir mai kula da shirye-shirye na kungiyar kwadagon ta Najeriya. |