|
Description:
|
|
Majalisun Tarayyar Najeriya sun koma bakin aiki, bayan daukar hutu na tsawon makwanni.
Majalisun dai sun shiga hutu ne bayan sauyin shekar da wasu daga cikin shugabanninsu suka yi daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP mai adawa, lamarin da ya haifar da jita-jitar dangane da yiyuwar tsige shugabannin majalisar daga mukamansu.
Bayan dawowa daga hutun kuwa, yanzu haka hankula sun karkata domin jin yadda za ta kaya.
Alhaji Abdulkarim Dayyabu, shugaaban rundunar Adalci, ya yi mana tsokaci dangane da fara zaman majalisun, yayin tattaunawarsu da AbdulKareem Ibrahim Shikal. |