|
Description:
|
|
Yau Talata 6 ga watan Nuwamba 2018, aka rantsar da shugaban kasar Kamaru Paul Biya wa’adi na 7, sakamakon nasarar da ya samu a zaben da ya gabata da kashi 71.
Shugaba Biya mai shekaru 85 da ya kwashe shekaru 36 a karagar mulki, yayi alkawarin tabbatar da gaskiya da kuma adalci a fadin kasar.
Shugaban ya kuma yi tsokaci kan ‘yan aware dake fafutukar raba kasar wajen tada hankali da kuma kaddamar da munanan hare-hare.
Dangane da sabon wa’adin Ahmed Abba ya tatauna da Dr Abubakar Ango, malamin Jami’a a kasar ta Kamaru. |